MUHIMMANCIN NEMAN ILIMI A MUSULUNCI

Annabi (S.A.W.) ya ce: "Neman ilimi wajibi ne a kan dukkan musulmi da musulma". Saboda haka ya kamata mu tashi tsaye wajen neman ganin mun sami ilimin da za mu bauta wa Allah Madaukakin Sarki, domin kuwa Yana cewa ka san ni kafin ka bauta min. Don haka matukar mutum yana raye neman ilimi a gare shi ba ya karewa na addini ko na zaman duniya domin cin ma wasu buƙatu na rayuwa, kamar su sanin kimiyya ko fasaha da makamantan su.

An karbo Hadisi daga Anas dan Malik Allah ya yarda da shi ya ce: "Na ji Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: Mai neman ilimi shi ne mai neman rahama, kuma neman ilimi yana daga cikin rukunan musulunci". Dailami shi ne ya ruwaito.

Wannan Hadisi yana nuna mana cewa rahama ba ta samuwa sai an samu ilimin nemanta a duniya, kuma shi kansa musulunci ba ya yiwuwa ga mutum sai yana da ilimin bautar Allah. Haka ita kuma rayuwa takan tafi a hagungunce ne ga jahili wanda ba shi da ilimin sanin yadda duniya da lahira ta dosa da kuma yadda za'a sami zama lafiya a nan duniya da ranar gobe ƙiyama.

An karbo daga Anas Dan Malik Allah Ya yarda da shi ya ce: "Annabi (S.A.W.) ya ce, mafi tsananin hasara da mutane ranar tashin ƙiyama su ne mutum wanda yana yiwuwa a duniya ya nemi ilimi bai nema ba, da mutumin da ya sanar da ilimi bai yi aiki da shi ba". Dan Askar ya ruwaito Hadisin.

Wajibi ne ga dukkkan muslmi ya tashi haiƙan tun yana kuruciyar sa ya nemi ilimin bautar Allah ba sai rayuwar sa ta kusa zuwa ƙarshe ba, wato lokacin da ya tsufa ya kasance yana mai danasani ko kokarin neman ilimi ba. Domin ita rayuwa tana da dama mai yawa, amma idan mutum ya bari damarsa ta neman ilimi ta kubce masa to daga ƙarshe ko ya tashi neman ilimin sai ka tarar yana yi masa wahala.

Ya Allah Ka ƙara mana ilimin bauta maka da sanin halin rayuwa, Allah Ka sa mu cika da imani da kalmar shahada, Ameen summa Ameen.

Share on Google Plus

About Unknown

    Blogger Comment
    Facebook Comment

2 comments:

  1. Allah ya saka da alkhairi ya bamu ilimi mai amfani.

    ReplyDelete
  2. @Asiya Gonto, Ameen!

    ReplyDelete